fidelitybank

Siyasa: Na yi hasashen dawowar Sanata Akume zuwa PDP – Iyorchia

Date:

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu ya yi hasashen dawowar ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume zuwa PDP.

Ya ce nan ba da jimawa ba ministan wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC a yankin Arewa ta tsakiya zai dawo PDP.

Ayu ya bayyana hakan ne a garin Gboko a lokacin da a ke shirin ficewar dan majalisar wakilai, John Dyeh daga APC zuwa PDP.

“Akume zai dawo PDP. Ina faɗin wannan magana bisa ga abin da na sani”. inji Ayu.

“A baya na annabci cewa Akume zai rike tsintsiya kuma ya yi. Yanzu ina annabata cewa zai dawo PDP. Idan ya dawo kar ka ki shi, amma ka tabbatar ka gyara shi, domin a inda ya ke a yanzu ba a tsaye ya ke tunani ba. Ya kasance ya rasa ɗan sa nahikaa. Sai dai a gyara masa sannan a tabbatar ya yi tunani da kyau,” inji Ayu.

Ayu wanda ya karbi bakoncin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka a majalisar wakilai ya ce, shi (Dyeh) ya ga hasken kuma ya yi alkawarin cewa za a yi wa duk wadanda suka sauya sheka adalci.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom ya yi maraba da dan majalisar tarayya da sauran wadanda suka sauya sheka.

Shugaban masu sauya shekar, Dyeh, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC ne saboda shugaban kasa kawunsa ne.

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sanatocin Arewa sun yi tir da kisan Zamfara

Ĉ˜ungiyar sanatocin Arewa, ta yi Allah wadai da kisan...

Tattalin arzikin Najeriya zai kara bunkasa a shekarar nan – IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta...

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ĉ˜ungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta kasa, ta fara...

Birtaniya ta na tsantsanr goyon bayam Hamas ne kawai – Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, matakin da Birntaniy...

Birtaniya ta gindaya wa Isra’ila sharuɗa

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya shimfiɗa wa Isra'ila wasu...

‘Yan Arewa su dakata da neman mulki har zuwa 2031 – Sakataren Gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, George Akume, ya yi kira...

Matatar Dangote ta janye Ĉ™arar da ta shigar kamfanin NNPCL a kotu

Matatar man Dangote ta janye Ĉ™arar da ta shigar...

Ba mu baiwa Obi shawara ya janye daga takara ba – Kungiyar Inyamurai

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide,...

Dole ne APC ta bar mana kujerar mataimakin shugaban kasa – ANPP

Tsagin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP...

Gwamna ya nada Sarkin Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin...

‘Yan Bindiga sun yi ikirarin kashe Daliban koyon aikin lauya a Benuwai

Ĉ³anbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun...

Tinubu ya gwangwaje tawagar Super Falcons da ruwan daloli da gidaje a Abuja

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bai wa Ĉ´an wasan...
X whatsapp