fidelitybank

Tsaro: Shugaban rundunar sojoji ya umarci Janar 50 su ajiye aikin su

Date:

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya (CDS), Janar Leo Irabor, ya umarci Janar-Janar 50 na rundunar sojin Najeriya da su mika takardar murabus dinsu nan take.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Post ya rawaito cewa, jami’an sun hadar da na rundunar sojojin saman Najeriya, sojojin kasa da kuma na ruwa; kusan 25 daga cikin manyan hafsoshi na cikin rundunar.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa Irabor ya bayar da umarnin ne a shelkwatar tsaro da ke Abuja ranar Litinin.

A taron da a ka yi da karfe 2:00 na rana, Irabor ya yi musu godiya bisa hidimar da su ka yi, kuma ya shaida wa duk wadanda suka halarci taron cewa lokaci ya yi da za su bar ofis.

Amma akwai wasu Course Janar 36  har yanzu suna da fiye da shekaru uku kafin su yi ritaya.

“Su kusan 50; biyu daga cikinsu a sojojin, za su yi ritaya a shekarar 2022, yayin da sauran kusan shekaru uku da rabi ne ya rage musu su kammala aiki,” inji majiyar.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Shettima ya yi wa iyalan marigayi Muhammadu Buhari ta’aziyya a Landan

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi wa wasu...

Indiya na jimamin mutuwar Buhari – Modi

Firaministan India Narendra Modi, ya shiga jerin shugabanni da...

Kungiyar Gwamnoni sun bayar da hutu kan mutuwar Buhari

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu...

Tinubu ya bayar da hutu don yin ta’azziyar Buhari

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan...

Shettima ya isa Landan domin dawo da gawar marigayi Muhammadu Buhari

A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim...

Najeriya ta yi rashin Buhari – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rasuwar tsohon...

Tabbas Buhari mutum ne mai kyakyawan halaye mai kishin kasa – IBB

Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya, Janar Ibrahim Babangida,...

Tabbas Buhari dan kishin kasa ne – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasa,...

Najeriya ta yi rashin Dattijo – Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana Muhammadu...

Buhari ya yi rayuwa mai sauki – Tajudeen

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abba ya miƙa ta'aziyyar...

A Daura za a yi jana’izar Buhari – Radda

Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce iyalan Muhammadu...

Ƴan Najeriya na cece-kuce dangane da rasuwar Muhammadu Buhari

Mutuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bar cece-kuce ga...
X whatsapp