fidelitybank

Siyasa: Buhari da kansa ya taya ni murna – Zago

Date:

Shugaban tsagin bangaren jam’iyyar APC a jihar Kano, Ahmadu Haruna Zago, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ahmadu Zago, wanda bangaren tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya zaba a matsayin shugaban jam’iyyar, ya gana da shugaban kasar ne a yayin da a ke ci gaba da rikici kan shugabancin APC reshen jihar ta Kano tsakaninsa da Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Rikicin ya samo asali ne bayan Sanata Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya sun balle daga bangaren Gwamna Ganduje inda suka zarge shi da rashin iya shugabanci.

Hakan ya sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar ta APC a watan Okotoban da ya gabata.

Rikicin ya kai su gaban kuliya kuma a hukuncin da wata kotun tarayya da ke Abuja babban birnin kasar ta yanke ta ce Ahmadu Zago ne halastaccen shugaban jam’iyyar ta APC.

Sai dai jam’iyar ta APC bangaren gwamnatin jihar Kano ta ce har yanzu ba ta karaya ba kuma za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace wajen ganin ta kwace shugabancin jam’iyyar.

A tattaunawarsa da BBC Hausa bayan ganawa da shugaban kasa, Ahmadu Zago, ya ce”Shugaba Buhari ya taya ni murnar yin nasarar samun shugabancin APC a jihar ta Kano”.

“Shi shugaban kasa ya tambaye ni ‘me a ka samu?’, ni kuma na ce masa ‘an samu shugabancin APC a Kano. Daga nan ne ya taya ni murna”, a cewar Ahmadu Zago.

Amma ya kara da cewa ba su tattauna kan rikicin da jam’iyyar ta ke fama da shi a jihar Kano ba, ya na mai cewa “Tun da batun ya na kotu ba mu tattauna a kansa ba. Ka san shugaban kasa ba ya shiga lamarin da ke gaban kotu.”

Da BBC su ka tambaye shi kan jita-jitar da ke cewa akwai yiwuwar su hade da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabi’u Kwankwaso, Ahmadu Zago ya ce “babu wannan batu. Sai dai ka san ita siyasa babu masoyi ko makiyi na dindindin.”

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp