fidelitybank

Ganduje ya yiwa Kwankwaso raddi kan zaɓen 2019

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi na cewa an yi magudi a zaben 2019 da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

PlatinumPost ta rawaito cewa, Kwankwaso, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, a wata hira da ya yi, ya zargi cewa Ganduje bai ci zaben gwamna ba, sai da karfi da ya ji a ka dora wa jama’a.

Sai dai wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce, sabanin ikirari na jagoran kungiyar ta Kwankwasiyya, Kwankwaso ya gudanar da wata hada-hadar magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, akasari ba sa yin zabe. hatta katin zabe ba su da shi an ba su damarar yin magudi.

Sanarwar ta ce a fili ya ke cewa, sa’o’i kadan da fara kada kuri’a a ka ce akasarin akwatunan zabe an cika su, sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance masu zabe ba ko kuma ba a tantace su ba. a cikin bayananta domin haka dole ne ta soke sakamakon daga cibiyoyi da yawa tare da ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Kwamishinan, a cikin sanarwar da PlatinumPost ta samu, ya yi nuni da cewa, abin takaici ne yadda a matsayinsa na shugaban da ke da hannu a cikin zaben, Kwankwaso har yanzu ya na ja da sakamakon zaben da hukumomi su ka gudanar da kotuna su ka amince da shi.

Kwamishinan ya ce, kwanaki kadan da su ka gabata, Kwankwaso ya kasance a kafafen yada labarai ya na gargadin mabiyansa kan kalaman da su ke yi, amma sai ya rinka yin kalaman da ba su dace ba.

Ya ce da alama, “Tattaunawar da Kwankwaso ya ke yi kullum, inda ya yi yunkurin lalata gwamnatin Ganduje ta yi masa illa fiye da alheri wanda kwata-kwata ya yi watsi da sulhun zaman lafiya da ya yi wa mabiyansa a ‘yan kwanakin nan” in ji kwamishinan.

Garba ya bayyana cewa, kamata ya yi Kwankwaso ya gode wa Ganduje bisa kammala ayyukan da ya yi watsi da su, inda ya ce al’ummar Kano na ganin kwaliyya na biyan kudin sabulu, saboda manufar ci gaba da ba ta misaltuwa da ta kai ga kammala ayyuka da dama a cikin shekaru shida da su ka gabata a jihar.

“Wadannan ayyuka sun hada da Aminu Dantata Flyover, titin Yahaya Gusau da Prince Audu Underpass, titin kilomita biyar a cikin kananan hukumomin Dawakin Tofa, Ungogo, Warawa, Rano da Tofa; Titin Mahmoud Salga, Titin Jaba-Rimin Kebe, aikin samar da wutar lantarki mai zaman kansa a madatsar ruwa Tiga da Challawa da dai sauransu.

Dangane da batun ilimi kuwa, kwamishinan ya bayyana cewa, dangane da ilimi gwamnatin Ganduje ta yi ayyuka da dama da su ka hada da biyan nauyin sama da biliyan 15 na tallafin karatu ga dalibai marasa galihu a kasashen ketare da gwamnatin Kwankwaso ta bari.

Ya ce ya zuwa yanzu an biya Naira biliyan 3.5 ga dalibai a Sudan; Naira biliyan 4.5 ga kasar Cyprus; Naira miliyan 384 ga wadanda ke Faransa, yayin da ake ci gaba da biyan dalibai a Masar da Indiya.

Malam Garba ya ce baya ga aiwatar da shirin na ilimi kyauta kuma wajibi na farko da na sakandare, gwamnatin ta samu damar gudanar da dimbin ayyukan raya ababen more rayuwa a dukkan manyan makarantunta da kuma ba da izinin kwasa-kwasan da suke bayarwa.

Sanarwar ta tabbatar da cewa, duk da yunkurin sulhun da a ke yi tsakanin shugabannin jam’iyyar, gwamnatin Ganduje za ta mayar da martani ga duk wani yunkuri na yin watsi da nasarorin da ta samu kuma ba za ta shagaltu ba za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da aka zabe ta ba ta aiwatar da su.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp