fidelitybank

Wadanda suka kakaba mana Ganduje su na da nasani – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada abun da ya sha faɗa a baya cewa, wasu manya ne daga sama su ka tursasa wa al’ummar Kano gwamnan da yanzu ya ke kan mulki, Abdullahi Umar Ganduje duk da cewa ya faɗi zaɓe a 2019.

Yayin wata hira ta musamman da jaridar Punch, Kwankwaso, ya ce, ”Na tabbatar yanzu wadanda su ka yi hakan suna da na sanin abun da su ka yi wa Kano. Duk jama’ar Najeriya sun san cewa Ganduje ya fadi zaɓen nan, amma haka su ka tursasawa mafi yawan jama’a ra’ayin wadanda ba su taka kara sun karya ba, wanda shi ne babban laifin da wani zai aikata”.

Ya ƙara da cewa”Abun takaici ne yadda wasu tsiraru su ka kasa ganin abun da talakawa su ka hango wa kansu.

”Mu na da ƙarin da iya hana su abun da su ka so yi a wannan lokaci, amma sai mu ka yi la’akari da cewa idan mu ka biye musu hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, domin haka mu ka bar su da aniyarsu, mu ka bi matakin shari’a, amma a nan ma a ka yi abun da a ka yi” inji Kwankwaso.

A halin da a ke ciki dai a na raɗe-raɗin sasantawa tsakanin tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Ganduje, bayan ziyarar ta’aziyya da Gandujen ya kai wa Kwankwaso.

dailypost news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...

Tsohon Ministan kuma jigo a PDP ya koma ADC

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda kuma sau uku a...

Trump ya caccaki Elon Musk

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon...

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki shiga jam’iyyar hadaka – Galadima

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...

Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar...

Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu a Najeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana...

Benue da Edo da Bayelsa na fargabar balewar madatsar ruwan Kamaru

Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon...
X whatsapp