Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, David Sassoli, ya mutu ya na da shekaru 65.
Mista Sassoli ya mutu da sanyin safiyar Talata a wani asibiti a gundumar Aviano na kasar Italiya.
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, David Sassoli ya mutu ya na da shekaru 65 a duniya.
Mista Sassoli ya mutu da sanyin safiyar Talata a wani asibiti a gundumar Aviano na Italiya, kamar yadda kakakinsa Roberto Cuillo ya tabbatar wa dpa.
A ranar Litinin majalisar dokokin EU ta tabbatar da cewa an kwantar da shi a asibiti a Italiya a ranar 26 ga Disamba “saboda wani mawuyacin hali na tabarbarewar tsarin rigakafi.
A watan Satumbar 2021, yayin babban taron majalisar, dan shekaru 65 ya zo da mummunan yanayin cutar huhu.
Mista Sassoli ya kasance shugaban majalisar EU mai kujeru 705 tun daga shekarar 2019.