An dawo da aikace-aikacen aika saƙon nan take na WhatsApp, bayan shafe sama da awa ɗaya da katsewa.
Da misalin karfe 8:20 na safiyar Talata, masu amfani da WhatsApp sun lura cewa ba za su iya karba ko aika sakonni ba, yayin da ba za a iya sabunta matsayin su ba.
Platinum Post Hausa, ta lura da cewa, jama’a daga wurare daban-daban suka yi ta amfani da manhajojin Twitter da sauran manhajoji don nuna rashin jin dadinsu a duniya baki daya.
Duk da haka, da karfe 9:45 na safe, an lura cewa masu amfani sun fara karɓar saƙonni, yayin da waɗanda aka aika suka nuna sun isa wurin da aka tura su.
Meta, mai WhatsApp, Instagram da Facebook, har yanzu bai bayar da wata sanarwa ba game da ci gaban.


