fidelitybank

SERAP ta mayar da martani a kan janye lasisin makarantun Kano

Date:

Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki ta Kasa ta mayar da martani game da janye lasisin makarantu masu zaman kansu da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi a jihar Kano.

A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta kwace lasisin gudanar da dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar.

Gwamna Ganduje ya dauki matakin ne biyo bayan kisan wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubukar da Abdulmalik Tanko, mallakin makarantar Noble Kids Academy da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar ya kashe ta.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Sunusi Sa’id Kiru, yayin da yake magana a ranar Litinin ya ce, za a sake duba lasisin da aka soke tare da sabunta su bayan an tantance su.

A martaninta, SERAP ta yi Allah-wadai da matakin, inda ta roki Ganduje da ya janye matakin, saboda hakan na iya kara ta’azzara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Kungiyar farar hula ta ce jihar Kano ce ta fi kowacce yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yanzu da 989,234.

SERAP ta bayyana hakan ne a shafin Twitter a yammacin ranar Talata.

Ta ce, “Muna kira ga gwamnan jihar Kano @GovUmarGanduje da ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa duk wasu makarantu masu zaman kansu na jihar ba bisa ka’ida ba.

“Kano ce ta fi kowacce yawan yaran da ba su zuwa makaranta (989,234).

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp