fidelitybank

Sake Fasali: El-Rufa’I zai kashe Naira biliyan 1.4 a makarantu jihar

Date:

Gwamnatin jihar Kaduna ta ware Naira biliyan 1.4 domin sake fasalin gina makarantu da shirye-shiryen samar da kayan aiki a fadin jihar baki daya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawai to cewa, aikin na daga cikin kasafin kudin shekarar 2021.

Wannan dai na kunshe ne a cikin kasafin kudi na shekarar 2022 na Naira biliyan 278.6 da gwamna Nasir El-Rufai ya sanya wa hannu a ranar Larabar da ta gabata, kuma ya bayyanawa manema labarai a Kaduna ranar Alhamis.

Takardar ta kuma nuna cewa daga cikin Naira biliyan 13.1 da a ka ware wa ma’aikatar ilimi domin gudanar da manyan ayyuka, za a kashe Naira biliyan 1.7 wajen sa baki, domin inganta abinci mai gina jiki a makarantun sakandare na kwana 26 da ke jihar.

Gwamnatin ta kuma ware Naira miliyan 658, domin gyara makarantun sakandire 69 a fadin jihar da kuma Naira miliyan 220, domin samar da kayan daki a makarantun sakandare.

Takardar ta bayyana cewa, za a kashe Naira biliyan 1.49 wajen gyara, kayan aiki da mayar da makarantu 16 a fadin jihar zuwa cikakkun wuraren kwana da kuma Naira miliyan 190.7 wajen sayo kayayyakin kimiyya da fasaha da kuma na sana’o’i.

Sannan ya nuna cewa za a kashe Naira miliyan 500 wajen siyan kayayyakin ilimi da litattafai, yayin da za a kashe Naira miliyan 10.4 wajen kafa da kula da lambunan makarantu a fadin jihar.

Hakazalika, an ware Naira miliyan 500, domin magance bala’o’i da gobara da iska, da ruwan sama a makarantun sakandare 50 da ke fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma ware Naira miliyan 20.3, domin gudanar da horon sanin makamar aiki da Jagora da masu ba da shawara a makarantu.

Za a kashe Naira miliyan 150 wajen bunkasa da tura tashar ilimi da kuma wadatar da dandalin ilmantarwa ta shafin internet.

Takardar ta kuma nuna cewa, an ware Naira biliyan 2.2 ga shirin tallafawa ‘yan mata matasa don koyo da karfafawa Bankin Duniya da kuma Naira biliyan 3.0 na hadin gwiwar Global Partnership for Education.

NAN ta rawaito cewa, Naira biliyan 13.1 da a ka ware wa ma’aikatar, domin gudanar da manyan ayyuka ya haura Naira biliyan 10.7 da a ka ware a shekarar 2021.

A cikin kididdigar kasafin kudi na Naira biliyan 278.6, an ware Naira biliyan 94.1 domin kashe kudade na yau da kullum, da kuma Naira biliyan 184.5 na kashe kudade, wanda ya nuna kashi 66.4 na jimillar kasafin kudin.

A cikin kasafin kudin, bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 69.8, wanda ya nuna kashi 25 cikin 100 da a ka ware biliyan 41.7, domin kashe kudi da kuma Naira biliyan 28 na kashe-kashe akai-akai.

 

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp