fidelitybank

Sabuwar Gobara ta sake kunno kai a Amurka

Date:

Wata gobara mai ƙarfi ta sake tasowa a yankin Los Angeles, wanda ta sa aka fara kwashe dubban mutane daga yankin zuwa wani wurin daban.

Gobarar ta taso ne daga kimanin tafiyar mil 45 wato kilomita 72 ta arewa maso yammacin birnin na Los Angeles a ranar Laraba, a kusa da tafkin Castaic mai tsaunuka da dama, kuma akwai gidajen mutane da makarantu a kusa.

Tuni wutar ta faÉ—aÉ—a zuwa faÉ—in murabba’in Æ™asa 10,000 a ranar Laraba saboda yanayin iska da buji da ake ciki, duk da cewa har yanzu ba ta kai ga cinye wani gida ko wurin kasuwanci ba, sannan mahukunta na cewa sun yi amannar kashe ta kafin ta munana.

Yankin ya sake faÉ—awa cikin shirin kar ta kwana ne saboda ganin yadda waccan wutar dajin ta É—aiÉ—aita jihar.

AÆ™alla mutum 31,000 ne aka ce tilas su bar yankin, sannan an yi wa wasu mutum 23,000 gargaÉ—in cewa akwai buÆ™atar su tashi daga yankin na Los Angeles, ciki har da fursunoni 500 da suma aka kwashe aka sauya musu wuri, kamar yadda wani jami’in tsaron, Robert Luna ya bayyana.

Shugaban hukumar kashe gobara ta Los Angeles, Anthony Marrone ya ce ma’aikatansa suna aiki tuÆ™uru domin shawo kan gobarar, inda ya ce, “mun kashe kusan kashi 15 na wutar zuwa safiyar Alhamis.”

Hukumomi a jihar na cewa wannan wutar ta bambanta da na’ukan wutar dajin da aka fuskanta kwanakin baya, inda aÆ™alla mutum 28 suka rasu, sannan sama da gidaje 10,000 suka lalace.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp