Majalisar wakilai na duba kudirin doka na neman samar da cancantar ilimi a manyan kujerun siyasar kasar nan.
Kudirin dokar da ‘yar majalisa daga jihar Ogun, Adewunmi Onanuga ta dauki nauyi ta zarce karatu na biyu a zaman majalisar na ranar Talata.
A halin da ake ciki, kudirin dokar da ba a tafka muhawara a kai ba, ta na neman a gyara sashi na 65, 106, 131 da 171 na kundin tsarin mulkin 1999.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa, kudurin dokar da ke neman gyaran kundin tsarin mulkin da ya tsallake karatu na farko a ranar Talatar da ta gabata, ya kuma nemi a kara mafi karancin cancantar ilimi kan masu neman kujerun gwamna da dan majalisar jiha da na tarayya.


