Rundunar ‘yan sandan jihar Delta na neman wani matashi mai suna Michael Ogbeife, dalibin ajin sakandire na SS3 dan makarantara Erhimu, Abraka a jihar ruwa a jallo.
Dalinin a na zargin sa da laifin dukan wani malamin makarantar, Joseph Ossai, har lahira a ranar Alhamis.
Marigayin malamin, wanda aka ce shi ne mai kula da kimiyyar noma da ilimin halittu a makarantar, har zuwa rasuwarsa, ya yi wa kanwar Michael bulala, mai suna Promise Ogbeife wadda ta samu sabani da abokin karatun ta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ce a yanzu haka su na nan sun baza komar su, domin kama matashin.