fidelitybank

Rundunar Soji ta saki sojan da ta amince da yin aure

Date:

Rundunar Sojin Najeriya ta saki wata Soja mai suna Sofiat Akinlabi da a ka tsare bayan wani namijin kokarin da ta yi a sansanin horar da matasa masu yi wa kasa hidima a jihar Kwara.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar.

Ya ce, “Zan iya tabbatar muku da cewa an ba da umarnin a saki sojan, kuma ya ji dadin bikin Kirsimeti tare da ‘yan uwa da abokan arziki tare da yi mata gargadi mai tsanani da kada ta sake yin irin wannan abu.”

Idan dai za a iya tunawa, rundunar sojin ta yi ikirarin cewa an tsare sojan ne, saboda ya saba wa dokokin soji da su ka haramta nuna soyayya ga jama’a da wani ma’aikacin jami’an tsaro.

Mai magana da yawun rundunar sojin wanda ya tabbatar da kamen makonnin da suk a gabata ya kara da cewa sojan ta saba ka’idojin rundunar sojin Najeriya kan yadda jami’an sojin ke gudanar da ayyukansu a lokacin da a ka tura su bakin aiki.

Nwachukwu ya ce ba a sa ran sojan macen za ta kasance da wata alaka mai ban sha’awa da wanda a ke horarwa; shiga cikin soyayya yayin da su ke sanye da kayan sawa, sannan kuma ya na da laifin kin bin umarnin rundunar soji na tsaye da kuma umarnin amfani da kafafen sada zumunta.

Tun a baya ne dai a ka ta matsa lamba a kan a saki soja mace wadda ta sumbaci masoyin ta a lokacin da ya amince zai aure ta a sansanin masu yi wa kasa hidima.

nigerianewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp