fidelitybank

Rikicin Siyasa: Malam Ibrahim ya ficce daga jam’iyar APC

Date:

Fitaccen malamin addinin musulunci kuma shugaban majalisar malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Da alama dai rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC reshen jihar Kano na yin mummunan tasiri a jam’iyyar yayin a cikin ‘yan kwanakin nan tun bayan da a ka fara samun tsagin shugabanci a cikin jam’iyar.

Malam Ibrahim ya bayyana ficewarsa daga cikin jam’iyar APC a cikin zantawarsa da BBC.

Ya ce,“To, a matsayina na dan APC kuma daya daga cikin dattawa kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar, ina so na tabbatar na fice daga APC,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

“Komai na rayuwa ya na da dalili. Dalilai uku ne: ko dai mai ilimi da hankali ya sa ni, ko kuma kowa ya sa ni, ko kuma shi kansa ya san dalili”.

Ya ce ficewar sa daga jam’iyyar ba ta da alaka da zargin da a ke yi masa na tsige shi a matsayin shugaban Majalisar Malamai.

“Idan da haka ne, da na sauka daga mulki. Ba dalili ba ne, domin kamar yadda ban yi bayanin rabuwata da gwamnati ba, ba sai na bata lokaci wajen bayyana ta ba.

“Ban daina siyasa ba kuma ban ce ba zan shiga jam’iyyar ba. Ni da kaina ban shiga ANPP ba, magoya bayana ne su ka yi min rajista. Domin haka yanzu zan shiga jam’iyyar da na ke so da kaina,” inji Malam Ibrahim Khalil.

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp