fidelitybank

Rikicin APC: Tsagin Ganduje ya kai karar tsagin Shekarau wajen shugaban ‘yan sanda

Date:

Jam’iyar APC reshen jihar Kano tsagin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sun rubuta takardar koke ga sufeto Janar na ‘yan sanda kan ayyukan da tsagin Malam Ibrahim Shekarau ke yi.

A cikin takardar karoafin mai dauke da sa hannun Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya da wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi 15 da kuma wasu shugabannin kananan hukumomi 15 na jam’iyyar APC, ta bukaci Sufetan ya binciki ‘yan siyasar da abin ya shafa tare da gurfanar da su gaban kuliya idan aka same su da su.

Wadanda aka lissafa a cikin koken sun hada da Sanata Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin, Nasiru Abduwa, Tijjani Abdulkadir Jobe, Sha’aban Sharada, Haruna Isa Dederi da kuma Ahmadu Haruna Danzago, wanda a ke yi musu lakabi da G7.

A cikin karar mai dauke da kwanan watan 6 ga watan Disamba, jam’iyyar APC karkashin jagorancin Ganduje ta zargi bangaren Shekarau da laifin haifar da tashin hankali, daukar nauyin tayar da hankulan jama’a, tayar da zaune tsaye, da rashin zaman lafiya, tashin hankalin jama’a da hargitsi a jihar Kano.

Jam’iyyar APC ta Kano ta kuma yi zargin cewa, bangaren Shekarau ya hayo wasu ‘yan baranda da aka yi amfani da su wajen yunkurin kwace sakatariyar jam’iyyar da injina a ranar 30 ga watan Nuwamba bisa zargin cewa wata babbar kotu da ke Abuja ta yanke hukunci a kan su.

Ga hoton kwafin wasikar.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp