fidelitybank

Rasuwa: Mu na mika sakon ta’aziyar mu ga iyalan Buhari Daura – Badaru

Date:

Gwamna jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya mika sakon alhininsa game da rasuwar, Alhaji Sani Buhari Daura.

PlatinumPost ta ruwaito cewa fitaccen dan kasuwar Alhaji Sani Buhari Daura ya rasu ne a ranar Lahadi ya na da shekaru 89 a duniya.

A sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin mai dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Habibu Nuhu Kila, gwamnan Badaru ya kuma jajantawa masarautar Daura bisa rasuwar Walin Daura.

Gwamna Badaru ya bayyana rasuwar, Alhaji Sani Buhari a matsayin babban rashi, ba ga iyalansa kadai ba, har ma da kasa baki daya.

Ya ce,”Marigayi Walin Daura ya yi rayuwa mai gamsarwa a matsayinsa na hamshakin dan kasuwa da al’ummar duniya da ba za a taba mantawa da hidimar da ya yi wa al’umma ba, mu na kuma yin addu’a Allah ya gafarta masa”. Inji Badaru.

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp