fidelitybank

Rashin neman amincewar gwamnati: Nyesom Wike ya kori kwamishinan lafiya

Date:

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya kori kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Princewill Chike, sakamakon rashin neman amincewar gwamnatin jihar na karbar bakwancin taron share fage na kungiyar likitoci da hakora ta Najeriya, MDCN, a Fatakwal, babban birnin jihar.

Gwamnan ya bayyana matakin da kwamishinan ya dauka na karbar bakwancin MDCN ba tare da izinin gwamnatin jihar ba a matsayin abin kunya ba.

Gwamna Wike ya sanar da korar Farfesa Chike ne a lokacin da Shugaban MDCN, Farfesa Abba Wasiri Hassan ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Fatakwal a ranar Litinin.

Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ba ta taba neman karbar bakwancin taron share fage na MDCN a Fatakwal ba, ya na mai jaddada cewa, kwamishinan lafiya ya yi kuskuren cewa bai shirya gudanar da taron ba a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kaddamar da ayyuka.

“A gaskiya ban taɓa ganin abin kunya irin wannan ba a rayuwata. Kowa ya san cewa ba dabi’a ba ce in kawo mutane kuma ba za ku iya halartan su ko bakwanci ba. Domin haka duk wanda ya yi haka zai sha wuya a kansa,” inji shi.

Wike ya kuma ce bukatar da MDCN ta yi na cewa gwamnonin jihohi su samar da manyan asibitoci guda daya a kowace karamar hukumarsu ta majalisar dattawa ba za ta cimma ruwa ba, saboda karancin kudade.

“Kun yi magana a kan samar da babban asibiti a kowace gundumar majalisar dattawa, kun san ba zai yi wu ba. Shi ya sa a Nijeriya muna da matsala. Lokacin da kuka je kasafin ku, kuna sanya kowane nau’in ayyuka. Ka san ba zai iya aiki ba. A ina za ku samu kudin da za a kafa wannan ayyukan a kowace gundumomin”. inji shi.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp