Babbar mai taimaka wa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan harkokin lafiyar al’umma, Uju Anwukah ta ce ƙasar ce ta farko a Afirka kuma ta biyu a duniya a yawan mutanen da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.
Hadimar Tinubun ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban kwamitin kula da ingancin abinci na Majalisar Wakilan ƙasar, Chike Okafor, wanda ya ce Najeriya na kashe dala biliya ɗaya da rabi a kowace shekara sakamakon matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Anwukah ta wadda ta yi magana kan inganta abinci ta ce ƙasar ƙoƙari ta wanan fanni ta hanyar ƙirƙiro da shirin N-774 da yanzu haka majalisar Wakilan ƙasar ta shirya taron ƙasa da ake gudanawar kan samar da wadataccen abinci mai gina jiki a ƙasar.
Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan da Ƙungiyar agaji ta ƙasar, Red Cross Nigeria ta ce akwai kimanin yara mliyan 5.4 da ke fama da uƙubar yunwa a jihohin ƙasar tara da ke fama da matsalar tsaro.