fidelitybank

Rashawa: Shugaban Malawi ya korfi kafatannin ministocinsa

Date:

Shugaban kasar Malawi, Lazarus Chakwera, ya kori dukannin ministocinsa, bisa zargin cin hanci da rashawa.

A wani jawabi da ya yi ga al’ummar kasar ta talabijin a ranar Litinin, shugaban ya lashi takobin tunkarar duk wata matsalar kin bin doka daga jami’an gwamnati.

Ya ce, za a kafa wata sabuwar majalisar ministocin cikin kwana biyu.

Ministoci uku na fuskantar tuhuma, wadanda suka hada da ministan kula da harkokin filaye, wanda aka kama a watan da ya gabata a kan zargin cin hanci.

Shi kuwa ministan kwadago ana zarginsa ne da karkatar da kudin yaki da annobar korona, yayin da ministan makamashi ke fuskantar zargin almundahana a kwangilolin mai.

Shugaban Malawai, Lazarus, ya na zargin kafatanin ministocin sa, wanda suka musanta zargin.

An zabi Mista Chakwera a shekarar 2020, inda ya yi alkawarin yakar cin hanci da rashawa.

A makon da ya wuce wasu kungiyoyin coci biyu masu karfin fadi a ji suka zargi shugaban da cewa ba ya kokari wajen yaki da matsalar cin hanci.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp