Rasha ta girke rukunin farko na makaman nukiliyarta a Belarus in ji shugaba Vladimir Putin.
Shugaban Rasha ya shaida wa mahlarta wani taro cewa za a yi amfani da su ne da zarar an yi wa Rasha ko iyakarta barazana.
Gwamnatin Amurka ta ce ba wata alama da ke nuna Rasha na son amfani da makaman nukiliyar don ta hari Ukraine.
“Ba mu ga wata lama ta cewa Rasha na son amfani da makaman ba,” in ji sakataren harkokin wajen Æ™asar Antony Blinken lokacin da yake tsokaci kan kalaman Putin.
Belarus babbar ƙawar Rasha ce, kuma Putin ya riƙa amfani da yankunanta lokacin da ya fara mamayar Ukraine a bara.


