fidelitybank

Rasha ta aike da dakarun soji zuwa Kazakhstan

Date:

Kasar Rasha ta aike da dakarun sojojin ta zuwa kasar Kazakhstan, domin taimakawa wajen kawo karshen tarzomar da ta barke a fadin kasar, bayan munanan tashe-tashen hankula da suka bazu a cikin tsohuwar gwamnatin Tarayyar Soviet.

‘Yan sanda sun ce sun kashe masu zanga-zanga da dama a babban birnin Almaty na tsakiyar yankin Asiya. Gidan talabijin din kasar ya ce, jami’an tsaro 13 ne suka mutu, ciki har da biyu da aka samu an yanke kawunansu.

Kamfanin dillancin labarai na Rueters ya rawaito cewa, wani gidan shugaban kasa da ofishin magajin gari da ke birnin, duk sun kone kurmus, sai dai ya zuwa yammacin ranar Alhamis, filin jirgin saman birnin, wanda masu zanga-zangar suka kwace tun da farko, ya na karkashin kulawar jami’an soji, yayin da motocin da suka kone sun cika titunan kasar.

Da sanyin safiyar Alhamis din nan, wasu dakaru masu sulke da dakaru da dama ne suka shiga babban birnin na Almaty, kuma a na jin karar harbe-harbe a lokacin da sojoji su ka tunkari taron, kamar yadda wakilan kamfanin dillancin labaran Reuters suka rawaito daga wurin.

 

dailysun

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp