Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce, sojin Rasha ba su janye daga birnin Kherson ba sai da suka tabbatar sun lalata dukkan ababen more rayuwa da ke birnin da kuma lalata na garuruwan da ke kusa.
“Kherson ya zama tamkar kufai, komai ya llace, babu wutar lantarki, babu ruwan sha, babu hanyar sadarwa, asibitoci da makarantu da wuraren shakatawa ma an lalata su,” a cewar shugaban.
Mateuz Lachowski, É—an jarida da ya kai ziyara Kherson, ya ce, abin da ya gani ya wuce na garin Bucha.
A cewarsa: “Na je Izyum da Burjanka da ke Bucha, an lalata su baki daya, amma Kherson ya sha bamban da sauran. Komai ya lalace. Wani abin tashin hankalin shi ne sojojin Ukraine sun haÆ™o sama da nakiya 2,000 da sojin Rasha suka binne.”