Majalisar Dattawa, ta ce, a ranar Litinin ta makon gobe ne za ta fara tantance mutanen da shugaban Bola Tinubu ya tura mata domin naɗawa a matsayin ministoci.
A ranar Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanto jerin sunayen mutum 28 waɗanda shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar domin tantance su.
Wannan dai ya zo ne bayan da ƴan ƙasar suka ƙagara su ji wadanda za su kasance ‘yan majalisar zartarwar sabon shugaban.
A tattaunawarsa da BBC, ɗan Majalisar Dattijan Najeriya, Sulaiman Kawu Sumaila, ya ce “Duk da dai ba a ƙarasa kawo sauran (sunayen) ba, amma za mu fara tantance 28 da aka gabatar a ranar Litinin mai zuwa, kuma tunda dole ne kowace jiha a samu minista, kamar yadda suka nuna shi ma sauran jerin sunayen ba da daɗewa ba za su gabatar mana da su.”
Sanata Kawu ya ce “Sako sunayen ƴan adawa a cikin jerin sunayen ministoci wani abu ne da zai sake samar da fahimtar juna, a yi aiki tare.”


