Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain, Neymar zai yi jinyar makwanni Takwas bayan da ya samu rauni a kafar sa.
Dan wasan na Brazil mai shekaru 29, an dauke shi ne a kan gadon marasa lafiya a ‘yan daf da a karkare wasan da suka doke Saint-Etienne da ci 3-1 ranar Lahadi.
Neymar na shirin buga wasanni bakwai na Ligue 1 na PSG da kuma wasan gasar zakarun Turai.
“Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa Neymar ya samu rauni a idon sawunsa na hagu da rauni,” A cewar PSG.