Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi na nan a cikin jam’iyyar har yanzu.
Yunusa ya bayyana haka ne a wajen taron ƙungiyar da aka yi a jihar Oyo, wanda aka tara ƴan siyasa da masana da ƙungiyoyin siyasa a jihar domin tattaunawa game da siyasar ƙasar.
Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito shugaban ƙungiyar yana bayyana hakan, inda ya ce, “domin warware shubuha da ake ciki, har yanzu Peter Obi ɗan Jam’iyyar Labour ne. Kun dai san akwai wasu matsaloli a jam’iyyar waɗanda ake jiran INEC ta kawo maslaha a game da su.”
Ya ƙara da cewa idan aka zaɓi Obi a matsayin shugaban Najeriya, “wa’aɗi ɗaya zai yi, kuma a wannan wa’adin ɗayan ne zai kawo canjin da ake buƙata. Yawancin matsalolin da muke fuskanta za a iya magance su a shekara ɗaya idan aka yi abun da ya dace. Kuma zai iya domin ya yi an gani a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.”