Hankali ya tashi a jihar Taraba yayin da mambobin jam’iyyar PDP, ke jiran hukuncin kotun koli kan dan takarar gwamnan jam’iyyar.
DAILY POST ta samu cewa za a yanke hukuncin ne a yau Juma’a.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kotun ta soke zaben fidda gwani na takarar gwamna da jam’iyyar APC ta gudanar.
Daya daga cikin ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Farfesa Jerome Nyameh ya garzaya kotun koli bayan da kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da ya shigar a kan dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Kefas Agbu, bisa hujjar cewa shi (Agbu) bai sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara ba.
Karanta Wannan: Zan ruguza PDP da ‘yan cikinta – Dan PDP a jawabin taron nnpp
Ya bayar da hujjar ta bakin lauyansa, Pius D. Pius cewa dan takarar shi ne shugaban jam’iyyar na jihar, wanda ya ce shi ne ya jagoranci tantance wasu masu neman tsayawa takarar mukamai daban-daban a dandalin jam’iyyar.
A lokacin shigar da wannan rahoto, tashin hankali ya mamaye sansanonin Agbu da Nyameh.
Wasu daga cikin magoya bayan nasu da suka zanta da DAILY POST, sun ce za su amince da sakamakon hukuncin da za a yanke cikin gaskiya.