fidelitybank

Orji Kalu ya bayyana burin sa na takarar shugaban kasa

Date:

Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

A zantawarsa da manema labarai ranar Talata a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, Kalu ya kuma yabawa kungiyoyin da su ka amince da shi ta hanyar lika hotunan yakin neman zabensa a fadin kasar.

Kalu ya ce, ya na shirin yin takara a matsayi na daya a kasar nan, idan jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da tikitin takarar shugaban kasa a yankin Kudu maso Gabas.

Tsohon gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa, jam’iyya mai mulki za ta samar da shugaban da zai yi aiki da hadin kan kasa.

Sai dai Kalu ya yabawa kungiyoyin da su ka tuntube shi, domin ya tsaya takarar shugaban kasa, kuma su ka same shi da ya cancanta ya samar da kyakkyawan shugabanci ga al’umma.

Ya ce: “Ina so in ci gaba da gode wa mutanen da su ke sanya hoto na a duk fadin Najeriya, ban yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa ba ko a’a.

“Amma idan an baiwa yankin Kudu maso Gabas dama, zan sake tunani in ga ko akwai hakan, domin jam’iyyar ba ta bayyana inda suka ware shugaban kasa ba.

“Amma na san jam’iyyar za ta kawo shugaban da zai yi aikin hadin kan kasa wanda ya fi muhimmanci.” A cewar Orji.

Sai dai Kalu, wanda ke komawa Abuja bayan hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara, ya bayyana cewa, ya na tuntubar masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa kan kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar.

Kalaman Kalu sun biyo bayan sanarwar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya yi na zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya tabbatar da cewa ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Da ya ke magana da manema labarai a fadar gwamnatin a ranar Litinin, Tinubu ya ce, bai sanar da ‘yan Najeriya burinsa ba, saboda har yanzu ya na tuntubar masu ruwa da tsaki.

 

 

 

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp