Rahotanni da ke ishe mu cewa, tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya, Cif Ernest Shonekan, ya mutu.
Cif Shonekan ya mutu ne a wani asibiti a birnin Legas ranar Talata, kamar yadda rahotannin suka nuna.
BBC ta rawaito cewa, Tsohon shugaban kasar ya mutu ya na da shekara 89 a duniya.
Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon kwaryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watabn Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.
Dan asalin jihar Ogun, an haifi tsohon shugaban kasar riko na Najeriya a watan Mayun 1936 a Lagos.
Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Lagos daga bisani ya tafi Landan don yin karatun digiri a fannin shari’a. Sannan ya ci gaba da neman ilimi a Jami’ar Harvard.
Ya daɗe yana aiki dsa kamfanin United Africa tun daga shekarar 1964, kuma ya riƙe manyan muƙamai a cikinsa.
Daga baya ya faɗaɗa harkokinsa a kasuwancin ƙasashen waje da kuma shiga harkokin siyasa.
A watan Janairun 1993 ne Cif Shonekan ya zama shugaba kwammitin miƙa mulki a ƙarƙashin shugabancin Janar Ibrahim Babangida.
A lokacin da yake kan mulkin Najeriya, Cif Shonekan ya saki fursunonin siyasa da Janar Babangida ya É—aure.