fidelitybank

Orji Kalu ya raba tallafin Babura da abinci da kudade a yankin sa

Date:

Bulaliyar majalisar dattijawa, Orji Uzor Kalu, ya bayar da tallafin Babura da kayan abinci tare da kyautar kudi ga al’ummar yankuna 13 na Igbere.

Tallafin dai wani yunkuri ne na ƙara ƙarin kayan aikin samar da tsaro a ƙauyena na Igbere.

Rabon tallafin kayayyakin wanda ya gudana a yammacin ranar Talata wanda Bulaliyar majalisar dattiawa mai wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar ta Tara, Sanata Orji Uzor Kalu ya ba da gudummawar Babura da kayan abinci da tsabar kuɗi ga al’ummomi 13 da su ka haɗa da Igbere.

An mika wadannan kayayyaki kai tsaye ga ‘yan banga a kauyen a gaban shugaban kungiyar jin dadin jama’a na Igbere, Comrade Goddswill .A. Okorie.

Babura da kayan abincin da Kalu ya rabawa al’ummar sa.

Idan kuma za a iya tunawa, Bualiliyar majalisar dattawa, ya duba ayyukan gina tituna sama da 50 a yankin Abia ta Arewa, kafin ya nufi Ezumezu, wajen wani kayan adana kayan tarihi na gargajiya da a ke gudanarwa duk watan Disamba a Igbere na jihar Abia.

Sanata ya kasance abin koyi na ci gaban al’umma. Ya wakilci mazabar Abia ta Arewa da kyau a Majalisar Dokoki ta kasa, a tarihin shekaru biyu da rabin da ya kwashe a zauren majalisar.

Kalu tare da mutanen da su ka samu tagomashin sa.

Mazabar Abia ta Arewa na matukar godiya da irin tasirin da ya ke da shi a fannin tattalin arziki, hadin kai da ci gaban ababen more rayuwa a fadin Abia ta Arewa.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...
X whatsapp