Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya gana da gwamnan Rivers, Nyesom Wike da wasu gwamnonin jam’iyyar PDP a jihar Ribas.
Taron dai shi ne karo na biyu da Obi zai gana da Wike bayan ya fice daga jam’iyyar PDP tare da bayyana aniyarsa ta shugaban kasa.
Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko ne ya bayyana ganawar Obi ta shafin Twitter.
Mimiko ya bayyana cewa an gudanar da taron ne a daren jiya.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da, tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke; tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwanbo; Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu; Mohammed Adoke da wasu da dama.