Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce, an yi garkuwa da jakadan kasar a Nijar a ofishin diplomasiyyar Faransa da ke birnin Yamai.
Mista Macron ya shaida wa manema labarai cewa halin da jakadan ke ciki abin damuwa ne.
Ya kuma ce sojojin na Nijar sun takura wa jami’an diplomasiyyar da ke zama a kusa da sansaninsu.
Tun cikin watan Agustan da ya wuce ne sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, suka bukaci jakadan na Faransa a Nijar ya fice daga kasar.
Bukatar da hukumomin Faransan suka yi fatali da ita, domin a cewarsu Shugaba Bazoum ne kadai ke ida ikon yin hakan saboda shi ne halastaccen shugaban kasa.
A wani labarin na daban kuma sojojin na Nijar sun bukaci dakarun Faransa 1,500 da ke kasar, da su fice daga kasar, bukatar da ita ma Faransa ta yi watsi da ita.


