Tsohon Ministan Sufuri kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Amaechi ya dage cewa shi ne gogaggen dan siyasar da zai riƙe Najeriya a duk fadin jam’iyyar don cike gurbin shugaban kasar nan a 2023.
“Ni ne dan Najeriya da ya fi kowa gogewa a kasar nan a yau a PDP da APC da ke neman wannan zabe. Na yi shekara takwas kakakin majalisa, gwamna shekara takwas da minista na shekara bakwai da kari.
Amaechi, wanda ya zama gwamnan jihar Ribas na wa’adi biyu, ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci tawagar yakin neman zaben sa don ganawa da wakilan jam’iyyar da kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC a Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Mai fatan zama shugaban kasa, ya bayyana cewa, ba wai yana neman a zabe shi ne bisa ra’ayin kabilanci ba, amma yana yin hakan ne a matsayinsa na wanda ya fi kowa cancanta, gogaggen dan Najeriya mai gaskiya da rike madafun iko.
Ya kara da cewa, zaman da ya yi a siyasance ta bangaren ‘yan majalisa da na zartaswa na gwamnatin jiharsa da kuma kwarewarsa a matsayin minista sun ba shi fifiko a kan sauran masu neman takara.