fidelitybank

Neman Sulhu: Turji ya nemi yin sulhu da gwamnati

Date:

Kasurgumin dan ta’addar nan da ya addabi wasu yankunan jihohin, Zamfara da  Sokoto da kuma Katsina, Bello Turji, ya nemi ya ajiye makamansa, domin a tsagaita zubar da jini daga dukkan bangarorin biyu.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Disamban 2021, Turji ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle da kuma Sarkin Shinkafi, kan bukatar tasa.

Wani mazaunin garin Shinkafi, wanda mamba ne a kwamitin zaman lafiya na garin, ya tabbatar wa da Aminiya sahihancin wasikar mai shafi uku a ranar Lahadi.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da dan ta’addar ke aike wa yankunan wasika ba. Ko a watan Satumban da ya gabata, ya rubuta wata wasika da shi da wani dan ta’addar, Halilu Sububu, su na gargadin mutane cewa za su kai musu hare-hare.

Neman sulhun nasa dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaron Najeriya suka zafafa kai hare-hare ga ’yan ta’addar ta sama da kuma ta kasa.

legit news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...

Luiz Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool...

NNPCL ya musanta sayar da matatar mai ta Fatakwal

Babban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya musanta...

Mun samu kuɗin gina titin jirgi daga Maiduguri zuwa Abia – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu duka kuɗin gudanar...

Sanatocin Arewa sun yi tir da kisan Zamfara

Ƙungiyar sanatocin Arewa, ta yi Allah wadai da kisan...

Tattalin arzikin Najeriya zai kara bunkasa a shekarar nan – IMF

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya sabunta...

Ma’aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Ƙungiyar ma'aikatan jinya da unguzomomi ta kasa, ta fara...

Birtaniya ta na tsantsanr goyon bayam Hamas ne kawai – Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, matakin da Birntaniy...

Birtaniya ta gindaya wa Isra’ila sharuɗa

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya shimfiɗa wa Isra'ila wasu...
X whatsapp