fidelitybank

Neja: ‘Yan ta’adda sun hallaka mutane 15 a lokacin da suke Sallah

Date:

Akalla mutane 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da a ka kai a wani masallaci a kauyen Ba’are da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da sallar Asuba.

Wata majiya ta ce an kai wadanda suka samu raunuka zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryas, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce akalla mutane 9 ne suka mutu a harin.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta riga ta tura jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya shafa, domin kara kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” inji Monday.

 

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya baiwa ‘yan wasan kwallon kwando dala dubu 100 da filaye a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta karrama kungiyar kwallon kwando ta mata...

‘Yan siyasa na kara matsin lamba Jonathan ya fito takara a 2027 – Bashir

Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa kan harkokin...

Gwamnati ta karbi tawagar ‘yan wasan kwallon kwando D’Tigress

Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando mata ta Najeriya ta...

Na ki marawa Atiku baya ne saboda juyin yankin Kudu ne – Wike

Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, a wata...

An saki sakamakon jarabawar WASSCE

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma ta fitar da...

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa wajen karbar abinci

Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra'ila sun sake...

Ambaliya ya shanye jihohin Bauchi da Filato da kuma Neja

Ambaliya ta cinye gonaki da gidaje da makarantu da...

Najeriya ta lashe gasar kwallon kwandon Afrika

Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe...

Obi ba zai iya lashe zabe a yankin Arewa ba – Keyamo

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya ce ɗaya...

Iya wa’adi daya ya ishe ni a mulkin Najeriya – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour, Peter...

Luis Diaz ya zaba wa kansa makoma da ya bar Liverpool – James

Kyaftin din Colombia, James Rodríguez, ya dage cewa dan...

Ka fito ka baiwa Matawalle hakuri ko ka fuskanci fushin kotu – Shinkafi

Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Dakta Suleiman Shuaibu...
X whatsapp