fidelitybank

NDLEA ta nemi hadin kan kasashen waje a kan shaye-shaye

Date:

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, Manjo janar Buba Marwa mai ritaya, ya ce, musayar bayanan sirri tare da karfafa hadin gwiwwa tsakanin kasashen Afirka zai taimaka wa kasashen nahiyar wajen yakar matsalar shaye-shaye da safarar miyagun kwayoyi.

Buba Marwa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen taron shugabannin hukumomin yaki da miyagun kwayoyi na nahiyar Afirka da ke gudana a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Yayin da yake jawabi game da nasarar da Najeriya ta samu wajen yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Buba Marwa ya ce ana bukatar hadin kan kasashen nahiyar wajen samar da hanyoyin da za a yaki dabi’ar safarar muggan kwayoyi a fadin kasashen nahiyar.

Ya kara da cewa tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022, NDLEA ta kama mutum 21,302 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ciki har da manyan diloli 28.

Haka kuma ya ce hukumar tasa ta kama miyagun kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogiram miliyan 5.4, tare da sauya wa fiye da mutum 12,326 masu amfani da kwayoyin tunani.

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp