fidelitybank

NDLEA ta kama kwayoyi mai nauyin kilo 12,285 da wata mata ‘yar shekara 70

Date:

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama tabar wiwi mai nauyin kilogiram 12,385, wani tarin ciyawar maye da aka shigo da ita daga wata kasa dake makwabtaka da jihar Legas ta hanyar ruwa.

Sanarwar mai kunshe da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Femi Babafemi ya sanyawa hannu tare da aiko ta zuwa ofishin PlatinumPost dake Abuja, sanarwar ta kuma ce cikin mutanen da aka kama akwai Abdulkadri Zakari mai shekaru 24 da Ka’abu Sausu mai shekaru 45 da kuma Lawrence Adie mai shekaru 27.

Bisa ga sahihan bayanan sirri ya nuna cewa an shigo da tabar wiwin mai nauyin kilo 12, 385 daga kasar Afirka ta Yamma ta cikin teku, kuma an yi jigilar su da jiragen ruwa zuwa Tekun Eko Atlantic, Victoria Island, inda za a rarraba su zuwa wuraren da dilolin ke da zama a Island, Peti Alagba da sauran su a fadin Legas da sauran jihohi.

Sama da jami’an  dake yaki da muggan kwayoyi 50 ne suka afkawa bakin tekun a ranar Asabar 27 ga watan Nuwamba, 2021, inda suka kwato kayayyakin tare da dogayen manyan motoci guda biyu, wata mota kirar Toyota Sienna tare da kama mutane Uku da ake zargi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, wata mata ‘yar shekara 70 mai suna Misis Beatrice Aigbedion na daga cikin wadanda aka kama a wasu sassan jihar Edo da laifin kama wasu miyagun kwayoyi da suka kai kilogiram 5,000 a fadin jihar.

Ko a ranar Larabar da ta gabata, an kama Misis Aigbedion ‘yar shekara 70 da maganin tari iri-iri na Codeine, Swinol da Rohypnol, yayin da wani dila mai suna Joseph Onyemaechi mai shekaru 50 kuma an kama shi a Ikpoba Okha, Upper. Sakponba- Birnin Benin, a ranar Juma’a mai dauke da nau’ikan sinadarai na psychotropic daban-daban masu nauyin kilo 2.055. Hakazalika, an kama Gabriel Akioya da Isa Salihu a ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba a Irrua, Esan Central LGA tare da nau’ikan Codeine, Tramadol, Swinol da Rohypnol.

A jihar Delta kuwa, jami’an tsaro sun kai samame a Hampton Towers da Spa Hotel, Okpanam Road, Asaba, inda aka kama Dobedient Etumudor da Thompson Chukwuemeka da wasu abubuwa masu guba, yayin da wani dillalin mai suna Emeka Ben aka kama da giram 4.7 na Methamphetamine a kan hanyar Asaba zuwa Ibusa. Sauran wadanda ake tuhuma da aka kama a ranar Alhamis 25 ga watan Nuwamba a jihar da laifin yin mu’amala a Meth, Cannabis, Cocaine, da Heroin sun hada da Ifeanyi Odibe, Uche Onwurah, da Justice Obika.

A jihar Kano kuwa, an kama wani dila miyagun kwayoyi, Alhaji Bukar Malan Abdu, tare da kwato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 143, yayin da aka kama kilo 466 na wannan magani a gidan wani Bashir Shu’aibu, dan asalin jihar Edo, amma mazaunin Kano, wanda ke sana’ar sayar da tabar wiwi. A ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, an kama wani dillalin kwaya a Maiduguri, jihar Borno, Chima Obi a wani samame da aka kai masa biyo bayan kama wani kayan kwaya mai nauyin kilo 73.2 na codeine, a wani shingen binciken hukumar NDLEA da ke Postiskum, jihar Yobe a ranar.

network news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp