Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wasu mutane 352 da ake zargi tare da kama tan 2.1 na haramtattun kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan NDLEA a jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na (NAN) a Kano ranar Alhamis.
Idris-Ahmad ya ce, an kama mutanen ne a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 208 da mata 44, yayin da magungunan da aka kama sun hada da kilogiram 955.304 na tabar wiwi, da Codeine da Tramadol kilogiram 1,225.05.
Sauran a cewarsa, sun hada da gram 25 na hodar iblis, gram 17 na tabar heroin da gram 52 na methamphetamine.
Kwamandan ya ce babban kalubalen da ke gaban hukumar a jihar shi ne shawo kan al’umma wajen bankado masu safarar miyagun kwayoyi a tsakaninsu.
“Kalubalen mu shine samun damar ilimantar da al’umma don samar da bayanai masu amfani game da maboyar masu amfani da muggan kwayoyi ko dillalan da ayyukansu suka ci gaba da yin illa ga al’umma.
“Ya kamata jama’a su lura da illolin da masu shan muggan kwayoyi ko masu safarar miyagun kwayoyi ke haifarwa a cikin al’umma ta yadda jama’a za su fito da bayanai masu amfani don tabbatar da al’ummar da ba ta da miyagun kwayoyi,” inji Idris-Ahmad.
Don haka ya yi kira ga jama’a da su rika bayar da bayanai masu amfani kuma a kan lokaci kan masu safarar miyagun kwayoyi ga rundunar, ta yadda za a fitar da su daga yawo da kuma kare al’umma.