fidelitybank

Nan da watan Maris zamu kammala tashar shigo da kaya a Kano – Bawuro

Date:

Shugaban tashar sauke kayayyaykin da ake shigo da su tsandauri ta Dala Inland Dry Port, Abubakar Bawuro, ya ce, kasuwanci tsakanin Najeriya da makwabciyarta ta Arewa, Jamhuriyar Nijar za ta samu ci gaba mai tarin yawa yayin da ake sa ran kaddamar da tashar a jihar Kano cikin watan Maris na 2022.

Ya ce, aikin wanda kawo yanzu ya lakume sama da Naira biliyan 5 na gine-gine ya kai sama da kashi 80 bisa 100 da aka kammala, tare da sauran ayyukan da ake sa ran za a yi nan da karshen watan Fabrairu na shirye-shiryen fara tashi.

Ya yin tattaunawa da magana labarai, a lokacin da ya ziyarci Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Mista Emmanuel Jime a Abuja.

A cewar Bawuro, “Muhimman wuraren ginin da suka hada da wurin da aka tara kwantenan tashohin ruwa a dakunan ajiyar kaya da guraben aikin gudanarwa da hanyoyin shiga da kuma samar da wutar lantarki a tashar, an yi su sosai. Idan ka duba su a ka tantance su gaba daya, za mu iya aminta da cewa mun kai sama da kashi 80 cikin 100 na kammalawa.

“Muna so mu tabbatar muku da cewa za mu yi aiki cikin awanni 24 a mako guda, domin ganin mun cimma burin ganin mun tabbatar da kuma kaddamar da tashar a karshen watan Maris”. In ji Bawuro.

Shugaban Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya, Mista Emmanuel Jime, ya yi alkawarin bayar da duk wani goyon bayan da ya dace, domin tabbatar da nasarar IDP na Dala.

 

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp