Adadin ɗanyen man fetur da Najeriya ke samarwa ya ragu da miliyan 2.3 a watan Yulin 2022, idan aka kwatanta da abun da ƙasar ta samar a watan Yuni daya gabata, bayanai daga Kungiyar matatar Mai ta Kasashe ta nuna a ranar Alhamis.
A watannin na baya-baya rahoton Kasuwar Mai na Agustan 2022 na OPEC ya bayyana cewa adadin danyen mai da Najeriya ke haƙowa ya nuna cewa ta fadi da kimanin ganga 74,000 a duk rana a wata Yuli.
Wannan yana nufin a kwanaki 31 a watan Yuli, ƙasar ta yi asarar kimanin miliyan 2.3 na gangar ɗanyen mai.
Bayanai daga OPEC sun nuna cewa hakar mai a Najeriya a watan Yuni 2022 da aka yi a duk rana an dinga samun ganga miliyan 1.158, amma ya fadi zuwa miliyan 1.084 duk rana a watan Yuli.
Kasar ta samar da ganga Miliyan 1.024 duk rana a watan Mayu na wannan shekarar, bisa ga adadin da OPEC ta saki Ranar Alhamis. In ji BBC.


