Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a daren jiya ya ce, Najeriya kasa ce mai sarkakiya, amma ba ta da wahala a iya tafiyar da ita idan ‘yan kasa na gaskiya.
Ya ce, mutum ba zai iya samar da hanyoyin magance kalubalen da kasar ke fuskanta ba, inda ya kara da cewa, ana bukatar hadin kan ‘yan Najeriya don magance matsalolin.
Obasanjo ya zanta da manema labarai jim kadan, bayan ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, da takwaransa na jihar Benue, Samuel Ortom, tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, wanda suka gana a gidansa da ke cikin babban dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL), Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Wike ya ziyarci tsohon shugaban kasar a ci gaba da tuntubar da yake yi a shiyoyin siyasa guda shida.