Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya yi kakkausar suka kan matakin da gwamnatocin ƙasashen Yamma suka ɗauka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza,
Mista Erdogan ya ce ƙasashen Yamma sun kasa ɗaukar matakan da suka dace don magance rikicin saboda jinin musulmai ake zubarwa.
Shugaban na Turkiya ya nuna shakku kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar kare haƙin bil-Adama ta duniya, yana mai cewa da alama ƙasashen yammacin duniya kan yi watsi da ita, idan ba ta dace da muradunsu ba, musamman idan ya shafi asarar rayukan musulmai.
A wani muhimmin mataki, Erdogan ya soke ziyarar da ya shirya zuwa Isra’ila tare da nuna nadamar yin musabaha da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York a watan da ya gabata.
Wannan yana nuna gagarumin sauyi a dangantakar diflomasiyyar ƙasashen biyu.
A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen gwamnatin Falasɗinawa, Riyad al-Maliki, wanda ke kula da Gaɓar Yamma da ƙogin Jordan, ba Gaza ba, ya bayyana hare-haren da Isra’ila ta kai a matsayin “yakin ɗaukar fansa.”
Da yake jawabi a kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasashen duniya da ke kasar Netherlands, al-Maliki ya jaddada cewa harin boma-bomai a Gaza na baya-bayan nan ya fi tsanani fiye da hare-haren da Isra’ila ta kai a baya, ya kuma yi kira a gaggauta tsagaita wuta.


