Kusan shekara 10 da suka gabata, James Howell ya jefar da ma’adanin bayanai na komfutarsa yayin da yake shara a gidansa, inda ya manta da kudin intanet na Bitcoin da ke cikinsa.
A yanzu da darajar Bitcoin ɗin nasa da ke ciki ya kai kusan fam miliyan 150, James na shirin kashe miliyoyin kudi domin haƙe wata ƙatuwar bola da nufin gano ma’adanin bayanan komfutar da ya ɓata. In ji BBC.
Mista Howell ya ce, in har ya gano ma’adanin bayanan na komfuta, zai bayar da kashi 10 na abin da zai samu don mayar da birnin zuwa cibiyar hada-hadar kudin intanet na crypto-currency.
Sai dai, mutanen yankin sun ce haƙo wurin zai jawo barazanar muhalli.
Tsausayi ne ya sa Mista Howell, wanda injiniya ne a fasahar sadarwa, ya jefar da ma’adanin a 2013, bayan samun kudin Bitcoin 8,000 a lokutan farko da aka ƙirƙiro da kudin.
Kudin Bitcoin ya samu tagomashi sosai a watan Janairun 2021, inda dukiyar Mista Howell ta kai fam miliyan 210, sai dai ya fuskanci karayar tattalin arziki a farkon wannan shekara.
Hukumar birnin da Mista Howell yake, wadda kuma ke da mallakin filin da ya jefar da ma‘adinan da kuma ya haƙiƙance yana ciki, ta hana masa damar tono wurin kan dalilai na barazanar muhalli da hakan zai kawo.
A yanzu Mista Howell ya yi alkawarin bayar da kashi 10 na kudin, muddin aka gano shi, domin tallafa wa ayyukan kudin intanet na crypto-currency.
Duk wani aikin da za a haƙa don gano ma’adinan bayanan na intanet, zai bukaci babban aikin hannu na tono dubban tan na ƙasa mai yawa da aka tara a wurin shekaru da yawa.
Amma Mista Howell ya yi imanin cewa a yanzu yana da kudaɗe da ƙwararru domin yin tono mai inganci da kuma ke da fa’aida ga muhalli.


