Hukumomi a Saudiyya sun kaddamar da sabuwar fasahar mutum-mutumi, domin hidimta wa Alhazai a masallatan Harami, cikin sabbin sauye-sauyen da aka bullo da su a bana.
Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa, an yi amfani da fasahar ne wajen rarraba wa Alhazai Alkur’anai a masallatan na Harami
Yayin da yake jawabi game da na’urar, Sakataren hukumar jin dadin Alhazan kasar Badr Bin Abdullah Al-Firaih ya ce na’urorin na iya shiga cikin taron jama’a ba tare da fuskantar wata tangarda ba.
Ya kara da cewa, mutum-mutumin na iya daukar kayan da nauyin su ya kai kilo giram 59, sannan suna da saurin tafiya.