fidelitybank

Mutum daya ya mutu 8 sun tsira da ransu a hatsarin kwale-kwale

Date:

Wani manomi, a ranar Lahadin da ta gabata, a garin Kabala Doki, dake karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna, ya nutse a cikin ruwa sakamakon hadarin kwale-kwale.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda wata majiya ta bayyana, yayin da wanda aka kashen mai suna Umar, ya taka kwale-kwalen domin taimaka wa mutanen da suka makale a gefen kogin amma kwale-kwalen ya kife.

Ya bayyana cewa wanda aka kashe din ya shahara a cikin al’umma kuma ya mallaki gona kusa da kogin.

Ya ce, “Abin damuwa ne domin Umar ya san yin iyo kuma ya yi noma a bakin kogi tsawon shekaru.

“Wannan ne ya sa muka yi mamakin samun labarin cewa ya nutse a cikin kogi daya a lokacin da yake kokarin ceto mutanen da suka makale a wancan gefen kogin. Allah ya gafarta masa kurakuransa”.

Majiyar ta bayyana cewa dukkan sauran da ke cikin jirgin sun tsira da ransu.

Shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Muktar Baloni, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa har yanzu ba a gano gawar mamacin ba.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp