Wasu mutum biyar sun rasa rayukansu yayin da suke kokarin tsere wa masu garkuwa da mutane a kauyen Chakumi na karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Cikin wadanda suka rasa rayukan nasu akwai maza biyu da mata uku, a wannan kauye da ke daura da kauyen Daku na karamar hukumar Gwagwalada.
Tabarbarewar matsalar tsaro ta kai ga wasu mazauna kauyukan da ke kananan hukumomin Abaji da Gwagwalada na yin kaura, suna barin gonakinsu babu masu kula da su.
Kamar dai yadda suka saba a wannan lokaci na damina, mutanen kauyen Chakumi da ke karamar hukumar Abaji ta babban birnin Najeriya Abuja, sun fita zuwa gonakinsu da sanyin safiyar ranar Laraba.
Sai dai bayan sun isa gonakin, sun hango masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai, lamarin da ya tilasta musu komawa gida.
Amma duk da sun koma gida – ba su tsira ba, domin masu garkuwa da mutanen sun bisu har kauyen nasu.
Cikin wadanda wannan al’amari ya rutsa da su akwai wata matar aure, baya ga wasu mutum biyu.
Abubakar Abdullahi, wanda tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji ne, ya shaida wa BBC cewa ‘yan uwansa biyu sun halaka a sanadiyyar kokarin tserewa masu garkuwa da mutanen.
Kuma Mallam Abdullahi ya shaida min cewa duk da kusancinsu da babban birnin tarayyar Najeriya, babu wani dauki da suka samu daga hukumimin birnin ko kuma jami’an tsaro.
Ya kuma ce har zuwa yau da rana ba a ga gawar wadanda ruwan kogin Gurara ya ci ba.
DSP Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja ta ce ba ta da cikakken bayani game da wanann harin da masu garkuwa suka kai, amma ta ce za ta bincika kuma za ta sanar da BBC abin da ta gano daga baya.
Matsalar tsaro a wannan yankin da ke kusa da kan iyakar Abuja da JIhar Kogi da kuma karamar hukumar Gwagawalada na kara tabarbarewa, har ya kai ga mazauna kauyukan na yin kaura zuwa wasu yankunan, inda manoma suka bar gonakinsu babu mai kulawa da su.