fidelitybank

Mutum 9 sun mutu 10 sun jikkata a wani hadari a Kano – FRSC

Date:

Hukumar kula da kiyaye hadura ta kasa. FRSC, ta ce hatsarin ya afku ne a lokacin da daya daga cikin motocin ya rasa yadda zai shawo kan motar bayan tsallake wani rami, sannan ya yi karo da daya motar.

Kakakin hukumar a Jigawa, Ibrahim Gambo, ya shaidawa PREMIUM TIMES cewa, tawagar ceto na hukumar ta kwato wadanda lamarin ya rutsa da su daga wurin kuma aka kai su asibiti.

An tabbatar da mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu 10 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ranar Litinin da ta gabata a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Hatsarin ya afku ne a wani yanki na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri da ake gyarawa kusa da kauyen Sabaru-Laraba da ke kan iyaka tsakanin jihohin Jigawa da Kano.

Jami’in ya ce, hatsarin ya rutsa da wata motar bas Toyota Hummer, mai lamba DRZ, 846, XA da kuma wata motar bas Toyota Sharon mai rijista Dal, 830, XA.

Jami’in ya ce, akwai maza 17 da mata biyu a cikin motocin biyu. Dukkan wadanda suka mutu maza ne, yayin da mata biyu na cikin wadanda suka samu munanan raunuka.

Da yake tsokaci kan hatsarin, mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, a wani sako da ya wallafa a Facebook, ya bayyana hatsarin a matsayin hadari mai muni.

Ahmad, wanda ya fito daga garin Gaya, ya ce, wadanda abin ya shafa ’yan unguwarsu ne, Gaya, wadanda suka je yawon bude ido.

Ya jajantawa Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim, shugaban karamar hukumar Ahmad Tashi, da iyalan wadanda lamarin ya shafa.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp