Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Bayelsa (BYSEMA), ta bayyana cewa akalla mutane casa’in da shida ne suka rasa rayukansu, inda jimillar mutane miliyan daya da dubu dari uku da arba’in da hudu da goma sha hudu suka shafa kai tsaye sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a jihar.
Wani bayanan hukuma da aka fitar a ranar litinin ya kuma nuna cewa, mutane miliyan daya da dubu dari biyu da goma da dari da tamanin da uku ne suka rasa matsugunansu.
DAILY POST ta tattaro cewa Yenagoa, babban birnin jihar, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 26 wanda shine adadi mafi yawa da aka samu ya zuwa yanzu.
Da yake tabbatar da bayanan, Shugaban Hukumar SEMA na Jiha, Hon. Walaman Igrubia, ya ce har yanzu ana ci gaba da tattara bayanai daga filin, yayin da yake lura da cewa ambaliyar ruwan ta shafi filayen noma da dama, gine-ginen makarantu, gine-ginen kiwon lafiya da dai sauransu.
Ya kuma tabbatar da cewa ambaliyar ta shafi al’ummomi da dama a daukacin kananan hukumomin jihar 8.
Igrubia ya bayyana karara cewa rahotannin farko da bayanan da hukumar SEMA da sauran hukumomi ke bayarwa sun nuna cewa jihar Bayelsa ce ta fi fama da ambaliyar ruwa a tsakanin Jihohin kasar nan.
Shugaban Hukumar ta SEMA ya bayyana cewa ya ji dadin jin cewa Ministar Harkokin Agaji, Gudanar da Masifu da Cigaban Jama’a, Hajiya Sadiya Farouq, yanzu ta amince da cewa Jihar Bayelsa tana cikin jerin Jihohi goma da suka fi fama da matsalar.


