Akalla mutum 11 ne suka mutu wasu tara kuma suka ji raunuka sakamakon wani hatsarin mota da ya auku ranar Asabar a daidai kauyen Hawan Jaki da ke Alkaleri a kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito babban kwamanda hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi na cewa hatsarin ya rutsa da motar daukar fasinja ta bas da kuma babbar motar daukar kaya ta kamfanin Dangote.
Ya kara da cewa bayan da hukumarsa ta samu labarin aukuwar hatsarin, jami’anta sun gaggauta zuwa wajen domin daukar wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin garin Alkaleri inda aka tabbatar da mutuwar mutum tara nan take, daga baya kuma wasu karin mutum biyu suka mutu.
Kwamandan ya kuma yi kira ga direbobi da su rika amfani da dokokin titi, tare da kauce wa gudun wuce-sa’a, musamman cikin watanni masu zuwa da za a samu yawaitar ababen hawa a kan manyan titunan kasar.