fidelitybank

Murnar cika shekaru 79: Idan n agama mulki zan koma gona ta – Buhari

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi bikin cika shekaru 79 a duniya a birnin Santambul ta kasar Turkiyya.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Garba Shehu, ya ce an yi bikin murnar cikar shekarun ne ta musamman.

A cikin wata sanarwa da PlatinumPost ta samu, Garba Shehu, ya ce: “A ranar cikarsa shekaru 79 a duniya, yau Juma’a a birnin Santambull ta kasar Turkiyya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanka Buredin “Cake” a kan zagayowar ranar haihuwar sa, mai launin kore-fari-kore, kai tsaye ya nufi kujera ya na shirin ganawa da jami’ai a cikin tawagarsa, sannan kuma ya wuce fadar Dolmabahce, domin ganawa da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan”.

A martanin karramawar da a ka yi a madadin ministoci da sauran tawagar da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya yi, shugaba Buhari, ya ce, zai yi iya bakin kokarinsa ga Najeriya har zuwa ranar karshe da za a yi zabe a 2023. Ya mika wa magajinsa ya koma gonarsa ya yi noma da kiwo.

Mai magana da yawun shugaban ya rawaito Buhari ya na cewa “Na yi tunanin cewa na yi nisa daga Abuja zan tsere wa wadannan abubuwa. Domin sun gaya mani abin da su ke son yi a wannan rana, sai ga shi yanzu a nan kuna yin wannan abun.

 

“Ina fatan shekarar 2023 idan na gama, in koma gida in ci gaba da aikin gona ta. Daga yanzu zuwa wancan lokaci, zan yi iya kokari na wajen ciyar da kasa da al’ummarta gaba, da gudanar da ayyuka na kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada”. Inji Buhari.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp