Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Afrika ta Kudu, a wani ɓangare na ziyarar da ya fara wasu ƙasashen nahiyar Afrika uku.
Mr Blinken zai gana da takwararsa Naledi Pandor, inda ake sa ran ya gabatar da sabon tsarin da Amurka za ta yi amfani dashi don kara samun ƙarfin faɗa aji a kasashen Afrika.
Dangantaka tsaƙanin ƙasashen biyu ta ragu a baya bayan nan, bayan da Afrika ta Kudu ta shiga sahun ƴan ba ruwanmu a yaƙin Ukraine. In ji BBC.
A dalilin haka Ms Pandor ta zargi Amurka da yunƙurin hukunta kasashen Afrika don kawai sun ƙi yin Allah wadai da kutsen Rasha cikin Ukraine.
Baya ga Afrika ta Kudu, Mr Blinken zai kai ziyara Rwanda da kuma Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.